Ƙungiyar Haɗin Kan Neman Ikon Mallakar Abinci a Afirka, wato AFSA, ta soki Bankin Raya Afirka, wato AfDB, kan yadda ya ke bai wa manyan kamfanoni tallafi a fannin noma. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da bankin, wanda ya zama shi ne mafi girma wajen samar da kuɗaɗe ga fannin noman a nahiyar, ya ke gudanar da manyan tarukansa na shekarar 2026 a Cibiyar Taro ta Kintélé da ke birnin Brazzaville. Sukan na zuwa ne a cikin wani rahoto da AFSA ta fitar tare da wasu ƙungiyoyi.
Dalilan sukar da AFSA ke yi
Ƙungiyar ta AFSA ta ce sukar da ta ke yi ta dogara ne kan wasu sababbin nazari guda uku da aka gudanar. A cewar Cibiyar Nazarin Talauci da Filaye da Noma, wato PLAAS, da ke Jami'ar Western Cape, an yi watsi da ra'ayin cewa Afirka na da filayen da ba a amfani da su ko waɗanda za a iya amfani da su wajen kafa manyan yankunan masana'antun noma. Ƙungiyar ta nuna cewa irin waɗannan filayen su ne tushen rayuwar al'ummomi da dama, kuma kwace su na barazana ga rayuwarsu tare da ƙara ta'azzara rikice-rikice kan filaye.
Haka nan, ƙungiyar ta AFSA ta yi nuni da cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tanada domin ayyukan da suka dace da yanayi wajen tallafa wa tsarin noman masana'antu mai zurfi da kuma noman amfanin gona iri ɗaya. Wannan tsari, a cewar ƙungiyar, ya saɓa wa manufofin yaƙi da sauyin yanayi da kuma tabbatar da wadataccen abinci, domin ya na ƙara gurɓata muhalli da rage nau'ikan amfanin gona da ake nomawa.
Halin da manoma kanana ke ciki
Rahoton ya jaddada muhimmancin da kananan manoma ke da shi a fannin samar da abinci a nahiyar Afirka, inda ya nuna cewa su ne ke kula da kusan kashi 80 cikin 100 na filayen noma. Su ne ke samar da kashi 80 cikin 100 na abincin da ake ci a yankin kudu da hamadar Sahara. Duk da wannan gagarumar gudunmawa da suke bayarwa wajen tabbatar da wadataccen abinci, ƙungiyar ta AFSA ta ce har yanzu kananan manoman ba sa samun tallafin da ya dace daga hukumomin kuɗi kamar bankin na AfDB. A maimakon haka, ana ba da fifiko ga manyan kamfanoni waɗanda ke amfani da hanyoyin noman masana'antu, wani abu da rahoton ya ce na barazana ga rayuwa da kuma ikon mallakar filaye na kananan manoma a fadin nahiyar.
Shawara da AFSA ta bayar
A matsayin hanyar da za a bi wajen magance matsalar, ƙungiyar ta AFSA ta gabatar da wani shiri mai matakai huɗu ga gwamnonin Bankin Raya Afirka. Ɗaya daga cikin muhimman shawarwarin da ta bayar shi ne a gaggauta dakatar da bai wa tsarin noman amfanin gona iri ɗaya tallafi a ƙarƙashin sunan ayyukan da suka dace da yanayi, wato ‘climate-smart’. Ƙungiyar ta ce irin wannan tallafin ya saɓa wa ainihin manufar yaƙi da sauyin yanayi.
Shirin ya kuma yi kira da a kafa wani asusu na musamman a cikin shirin nan na 'Feed Africa' da bankin ya ƙirƙiro. Manufar wannan asusu ita ce tallafa wa tsarin noma mai sauƙi wanda ba ya buƙatar amfani da sinadarai masu yawa, da ayyukan da ke inganta lafiyar ƙasa, da kuma farfaɗo da amfani da irin gargajiya. Haka nan, shawarwarin sun haɗa da buƙatar kare tsarin amfani da irin da kananan manoma suka gada, wanda ke da muhimmanci ga tabbatar da nau'ikan amfanin gona da kuma ikon mallakar abinci a nahiyar.
Babban tambaya da ake yi
Ƙungiyar ta AFSA ta ce dabarun bankin na AfDB na raba kuɗaɗe a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2025 sun fi karkata ne wajen tallafa wa kamfanoni masu zaman kansu da manyan harkokin kasuwancin noma na duniya. Saboda haka, taswirar da ƙungiyar ta gabatar ta buƙaci bankin ya fito da cikakken bayani kan waɗanda suka amfana da kuɗaɗensa, tare da tabbatar da an mutunta haƙƙin mallakar filaye na gargajiya.