BCEAO Ta Tilasta Amfani da Sabon Tsarin Biyan Kudi na PI-SPI

Hoto ta Anp

Babban Bankin Kasashen Yammacin Afirka (BCEAO) ya sanar da fara aiki gadan-gadan da kuma tilasta yin amfani da sabon tsarin biyan kuɗi na PI-SPI a ranar 2 ga Nuwamba, 2026. Wannan mataki ya mayar da amfani da dandalin wajibi ga cibiyoyin hada-hadar kuɗi da ke yankin, domin gudanar da hada-hadar tura kuɗi tsakanin ɓangarori daban-daban.

Sabuwar hanyar tana aiki ne kai-tsaye a kan dukkan ayyukan tura kuɗi tsakanin kamfanonin wayar salula na MTN, Orange, Moov, da Wave, tare da hada-hadar kuɗi da ake yi tsakanin waɗannan kamfanoni da kuma bankuna.