Burkina Faso Ta Kaddamar Da Sabon Tsarin Yadin Da Kebe Da Kimanin Naira Biliyan 17

Burkina Faso : Ibrahim Traoré inaugure TEXFORCES-BF, un complexe textile de 17 milliards FCFA
Hoto ta Lesechosduniger

Shugaban ƙasar Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, a ranar Laraba 9 ga watan Satumbar 2026, ya kaddamar da babban kamfanin sarrafa yadi na rundunar sojin ƙasar, wato TEXFORCES-BF, a birnin Bobo-Dioulasso. An gina wannan masana'anta ne a yankin Logofourousso da ke ƙarƙashin gundumar Guiriko. Gwamnatin ta ce an zuba jari na kimanin CFA biliyan 17 wajen gina wannan katafaren kamfani. An kafa wannan masana'anta ne da nufin farfaɗo da masana'antun sarrafa auduga da bunƙasa tattalin arzikin ƙasar ta hanyar samar da kayayyakin da ake buƙata a cikin gida.

Ikon Samarwa Da Ayyukan Da Aka Samar

Masana'antar TEXFORCES-BF tana da karfin sarrafa audugar da ta wuce tan 12 a kowace rana. A matakin da take yanzu, ana sa ran wannan katafariyar masana'anta za ta samar da guraben ayyukan yi kai-tsaye kusan 600, da kuma wasu guraben ayyuka 15,000 a kaikaice, waɗanda suka haɗa da manoma da masu jigilar kayayyaki.

Hukumomi sun bayyana cewa, a kowace shekara, masana'antar tana da ikon samar da yadika da tsawonsu ya kai mita miliyan 20. Baya ga haka, za ta iya samar da kakin sojoji miliyan shida, da T-shirt miliyan shida, da kuma safa miliyan ɗaya. Wannan mataki na daga cikin kokarin da gwamnatin ke yi na bunkasa tattalin arzikin cikin gida da kuma rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje.

Manufar Gwamnati A Samar Da Kayayyakin

Kafa masana'antar ta TEXFORCES-BF na daga cikin manufofin gwamnatin Burkina Faso na ƙara sarrafa albarkatun cikin gida. Wannan mataki na da nufin rage shigo da kayayyakin yadi daga ƙasashen waje, lamarin da zai taimaka wajen dakile yawan fitar da kuɗaɗen ƙasar zuwa waje. Gwamnati ta bayyana cewa, ta hanyar sarrafa audugar da ake nomawa a cikin ƙasar, za a samar da kayayyakin da ake buƙata na yau da kullum, ciki har da kakin sojoji da na sauran jami'an tsaro. Wannan dabarar na daga cikin shirin ƙasar na dogaro da kai, inda ake son a ƙarfafa kamfanonin cikin gida su samar da mafi yawan buƙatun al'umma, maimakon a ci gaba da dogaro da shigo da kaya daga ketare, wanda ke ci wa tattalin arzikin ƙasar baya.

Tsarin Dogon Zango Na TEXFORCES-BF

A cikin dogon zango kuwa, masana'antar ta TEXFORCES-BF na da burin kaiwa ga sarrafa tan dubu 50 na auduga a kowace shekara. Idan aka kai ga wannan mataki, ana hasashen za ta iya samar da yadi mai tsawon mita miliyan 100, da kuma wasu kayayyaki da aka gama sarrafawa da yawansu ya haura miliyan 20. Wannan wani babban mataki ne da ake sa ran zai ƙara faɗaɗa tasirin masana'antar a fannin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar.

Dangane da samar da ayyukan yi, hasashen da aka yi na dogon lokaci ya nuna cewa masana'antar za ta iya samar da guraben ayyuka kai-tsaye har dubu 20. Baya ga wannan, ana sa ran za ta samar da wasu ayyuka da hanyoyin dogaro da kai kusan dubu 60 a cikin dukkanin sassan da suka shafi auduga, tun daga nomanta har zuwa kai ta kasuwa.