Firaministan Nijar ya karbi jakadan musamman daga kasar Senegal

Image 1
Hoto ta Anp

Firaministan ƙasar Niger, Ali Mahaman Lamine Zeine, ya karɓi baƙuncin wani jakadan musamman da shugaban ƙasar Senegal ya aiko zuwa gare shi.

Ganawar ta gudana ne tsakanin Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine da wakilin na shugaban ƙasar Senegal domin tattaunawa a kan batutuwan da suka shafi dangantakar ƙasashen biyu.