Kaddamar da shirin 'Une semaine, une école' a yankin Diffa

An ƙaddamar da shirin nan mai taken 'Une semaine, une école' a yankin Goudoumaria da ke cikin jihar Diffa. Wannan shiri ya mayar da hankali ne kacokan wajen cusa dabi'un kishin ƙasa tare da ɗaga daraja da ingancin koyarwa a makarantu.