Fitaccen mawaƙin ƙasar Nijar, Mahamadou Bado, wanda aka fi sani da Maidawa, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 72 a duniya. Mutuwar wannan mawaƙi ta girgiza masana'antar fasaha da al'adun ƙasar ta Nijar da kuma ɗaukacin masoyansa.
Mahamadou Bado, wanda sunan Maidawa ya zama babban tambari a fagen waƙoƙin gargajiya da na zamani a ƙasar ta Nijar, ya rasu ne bayan ya shafe shekaru da dama yana bayar da gudunmawa wajen raya al'adu da faɗakar da al'umma ta hanyar fasaharsa ta waƙa. Labarin mutuwar tasa yana ci gaba da sosa zukatan mutane daban-daban a faɗin ƙasar.