Yaki da Miyagun Kwayoyi: An kama mutane da dama a Niamey

A ranar Asabar, 15 ga watan Agustan 2026, hukumomi a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar sun gudanar da wani sumame da ake kira 'Tamisée', wato 'Hagay' da Zarmanci ko 'Tankaday' da Hausa. Wannan shi ne karo na bakwai da ake gudanar da irin wannan aiki, wanda babban manufarsa ita ce ƙarfafa yaƙi da safara da kuma shan miyagun ƙwayoyi. A yayin aikin, an gano direbobi 25 sun sha abubuwa masu sanya maye. Haka nan an kai mutum 49, ciki har da mace ɗaya da yara ƙanana uku, zuwa hukumar OCRTIS bisa zargin laifukan da suka shafi ƙwayoyi.

Yadda Ayyukan Ya Gudana

Aikin ya gudana ne a matakai guda uku.Aikin ya gudana ne a matakai guda uku. Matakin farko ya haɗa da duba lafiyar direbobi da sauran masu amfani da hanyoyi a wurare daban-daban da kuma ta hanyar sintiri. Mataki na biyu kuma shi ne sintiri a yankunan gundumomi biyar na birnin Yamai. Mataki na uku kuwa shi ne sintirin ruwa a gefen kogin Nijar. An yi wa direbobi 182 gwajin shan kwayoyi. Daga cikin abubuwan da aka gano sun sha akwai wiwi, da tramadol, da kuma wata kwaya mai suna ecstasy. Haka nan an gano wasu sun sha sinadaran morphine da amphetamine. Direbobin da aka samu da laifin shan wadannan kwayoyi suna tuka manyan motoci kirar Hiace da manyan tireloli da motocin haya na tasi da bas-bas, da kuma babura masu kafa uku da ake kira adaidaita sahu.

Sakamakon Kama da Kwatancen

A yayin matakai na biyu da na uku na aikin 'Tamisée', an cafke jimillar mutane 306. Daga cikin waɗanda aka kama akwai maza 266, da mata 15, da kuma yara ƙanana 25. Wannan adadi ya shafi waɗanda aka kama ne a yayin sintiri a gundumomin birnin Yamai guda biyar da kuma waɗanda aka kama a gefen kogin Nijar. Bayan an tantance su, an miƙa mutane 257 ga sauran sassan jami'an tsaro domin a yi musu bincike kan wasu laifuka da suka shafi hurumin waɗancan sassa. A cikin wannan rukuni na mutum 257 akwai mata 14 da yara ƙanana 22. Gabaɗaya, adadin mutanen da aka kama a dukkan matakai uku na aikin ya kai mutum 331. Cikin wannan jimilla, an samu maza 291 da mata 13, sai kuma yara ƙanana 27. Wannan ya haɗa da direbobin da aka kama a matakin farko da kuma waɗanda aka kama a sauran matakai biyu na sintiri a ƙasa da kuma a ruwa.

Abubuwan Da Aka Kama

A yayin wannan aiki, hukumomin sun ƙwace ƙwayoyin benzhexol guda 10,500, da ƙullun wiwi guda biyar, da kuma naɗaɗɗen wiwi guda huɗu. An kuma samu wasu naɗaɗɗun guda 11 na daban, tare da ƙwayoyin tramadol guda 532. An yi nasarar tattara waɗannan abubuwa a wurare daban-daban da aka kai samamen.

Sauran kayayyakin da aka samu sun haɗa da babura guda 17, da buhu ɗaya na wani foda, da na'urorin shan taba-ruwa guda biyu tare da buhunan kayan shan taba-ruwan guda biyu. Har ila yau, an ƙwace wasu magungunan asibiti, da talabijin guda ɗaya, da jakuna biyu na ɗaga mota, da kuma wata kayar kiɗan gargajiya guda ɗaya.

Manufar Ayyukan

Babban jami'in hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta OCRTIS ya bayyana cewa manufar wannan sumame ita ce su durƙusar da masu safarar ƙwayoyi. Ya ƙara da cewa suna kuma son su kawar da dukkan masu aikata laifuka a wuraren da aka san sun yi kaurin suna a birnin Yamai.