Kamfanin Blueberry Travel and Tourism ya bude sabon ofishinsa a Yamai

Hoto ta Anp

Ministar yawon buɗe ido da sana’o’in hannu ta ƙasar Niger, Guichene Kari Aghaichata, ta buɗe sabon ofishin kamfanin Blueberry Travel and Tourism a birnin Niamey a ranar 19 ga Oktoba, 2026.

Buɗe sabon ofishin na Blueberry Travel and Tourism yana da nufin ƙarfafa alaƙar sufuri da mu’amala ta ƙasa da ƙasa ga Niger, tare da bayar da gudunmawa wajen bunƙasa ɓangaren yawon buɗe ido na cikin gida.